Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {a.s} - ABNA - habarta cewa, jami’an gwamnatin haramtacciyar kasar Isra’ila tare da goyon bayan sojojin yahudawan sahyoniya sun rusa gidan wani mazaunin unguwar Sheikh Jarrah da ke birnin Kudus da suka mamaye cikin dare ga kuma Yanayin sanyi, tare da kama shi da iyalansa. Sojojin yahudawan sahyoniya sun tsare dukkanin iyalan Mahmoud Salehieh, ciki har da wani yaro dan shekara 9, kafin su ruguza gidan. Inda Tsawon watanni da suka gabata gwamnatin yahudawan sahyoniya ta na tilastawa mazauna wannan unguwa da kuma mika gidajensu ga sahyoniyawan, wanda a watan Mayun da ya gabata ya haifar da kazamin fada a cikin yankin da kuma martanin kungiyoyin gwagwarmaya a Gaza, inda aka kwashe kwanaki 11 ana yakin. Wannan batun dai shine abunda wannan zane mai ban tausai ke dauke da shi wanda jaridar Al-Quds Al-Arabi ta kasa da kasa ta fitar.